Shugaban ya kai ziyarar kaddamar da ayyuka a jihar Kaduna yau Alhamis 4 ga watan farko na 2018.
A cewar shugaban "masu yin kasuwanci a kan tudu sun jima suna jiran a bude irin wannan tashar wacce za ta saukaka yadda ake kasuwanci a kasar".
An kiyasta cewa za ta dauki kusan ton dubu talatin na kago a shekara, kuma za ta kasance cibiyar rarraba kayayyaki a arewacin kasar har ma watakila zuwa kasar Nijar da Chadi.
Gwamnatin tarayya na sa ran bude wasu karin tasoshin ruwan na kan tudu guda shida a garin Ibadan, Aba, Kano, Jos, Funtua da Maiduguri.
Kafin ya kaddamar da tashar ruwa ta kan tudu shugaban ya fara kaddamar da sabin karin na'urar jigilar jama'a ta jirgin kasa a nan tashar dake garin Rigasa na jihar.
Manyan baki da suka ziyarci jihar Kaduna tare da shugaban sun hada da Gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje, ministan sufuri Rotimi Ameachi da babban sufeton yan sanda Ibrahim Idris.