Advertisement

Yar shekara 15 ta tsere daga hannun yan ta'adda

Dakarun 28 task force suka gano ta bayan ta kubuta daga hannun yan ta'adda.
Advertisement

Sojoji sun gano wata yar shekara 15 tayi nasarar kubucewa daga sansanin mayakan boko haram dake garin Gubla nan jihar Adamawa.

Advertisement

A bayanin da kakakin rundunar sojojin Nijeriya Birgediya Janr Texas Chukwu yayi, yace dakarun 28 task force suka gano ta ranar lahadi 29 ga watan Yuli.

Kamar yadda suka gano sunanta Zainab Mohammed  kuma sojojin zasu mika ta ga hukuma bayan kammala bincike.

Mai magana da yawun rundunar ya kara da cewa sojojin sunyi nasarar dakile wani hari da mayakan ke shirin kaiwa kuma sun gano bindigar AK-47 tare da kunshin harsashin bindiga.

Advertisement
Latest Videos
Advertisement