Advertisement

Sabin fina-finai da ya kamata ku kalla a bikin sallah

Ana iya zuwa sinimu domin kallon su ko kuma a garzaya kasuwa domin siyan su.
Advertisement

Gabanin bikin babban sallah wanda zata fara ranar Talata 21 ga watan Agusta, ga wasu fina-finan hausa na dandalin kannywood da suka ya kamata a kalla.

Advertisement

Ana iya garzayawa sinimu ko wuraren kallo tare da iyali, yan uwa ko abokan arziki domin kallon kayatattun sabbin fina-finan.

Mujadala

An sake shirye tsohon shirin wanda ya aka shirya tun shekarun baya. Kamfanin Mai shadda Investment ta shirya kuma jaruman da suka fito a cikin sun hada da Ali Nuhu, Maryam Yahaya da Umar M.Shereef.

Mariya

Advertisement

Kamfanin Mai shadda Investment ta fitar da kayatatcen shirin fim ga kasuwa. Maryam Yahaya da Umar M.Shereef sun taka rawar gani a cikin.

Sarauniya

Shararren mai bada umarni Hassan Giggs ya bada umarni a wannan shirin inda Ali Nuhu daAdam A.Zango suka nuna jarumtaka tare da Asabe Madaki da Hannatu Bashir. Sani Sule Katsina ya shirya ta.

Fuska Biyu

Fuska biyu shiri ne wanda labarinta ya sha bambam da sauran fina-finan hausa da aka saba gani. Ta bada labarin rayuwar zama dan arewa da kuma yadda daukar mataki ke haifar da sakamako mara dadi. Kamafanin Uk Entertainment ta shirya kuma sannanen direkta Yaseen Auwal ya bada umarni. Jaruman da suka fito a cikin ta sun hada Adam A.Zango, Falalu Dorayi, Alhassan Gwale, Halima Atete da Hajara Usman.

Advertisement
Advertisement
Latest Videos
Advertisement