Advertisement

Gwamnatin jihar Jigawa ta karya farashin shinkafa ga ma'aikatan ta

Ta rabawa ma'aikatan jihar da shinkafa cikin farashi mai rahusa wanda zasu biya cikin wata biyu.
Advertisement

kamar yadda majiya Rariya suka ruwaito, gwamnatin jihar ta bada wannan shinkafar ga ma'aikatan kananan hukumomin jihar kan farashin naira dubu goma sha biyu tsabanin dubu sha huda da ake siyarwa a kasuwa.

Advertisement

Gwamna Abubakar Badaru ya dauki wannan matakin ne domin taimakawa al' ummar jihar samun yin azumi cikin nishadi da walwala.

Ya kuma yi alkawarin biyan dukanin ma'aikatan jihar kudin hutun su cikin lokaci domin su samu su tafiyar da tsabgogin yau da kullum.

Advertisement
Latest Videos
Advertisement