Advertisement

Dan kasuwa bai fidda rai wajen siyan kungiyar Arsenal, ya bada lokaci da zai dauki matakin yin haka

Tun ba yau ba attajirin wanda shine mafi kudi a nahiyar Afrika ya sanar da sha'awar siyan kungiyar take taka leda a gasar firimiya ta Ingila.
Advertisement

Shahararren attajirin dan kasuwa Alhaji Aliko Dangote tsaya kan bakan sa na siyan sanannen kungiyar kwallon kafa ta Arsenal dake Ingila.

Advertisement

A wata hira ta musamman da yayi da wakilin BBC, Dangote ya shaida cewa yunkurin siyan kungiyar tana nan sai dai amma za'a fara daukar matakin cikin shekarar 2020.

Yace a halin yanzu akwai wasu muhimman ayyukan da ya tasa a gaba wanda sai bayan ya kammala su zai bude wanann shafin.

"Yanzu muna da abubuwa muhimmai , kamar su matatar mai, kamar su kamfanin taki, kamar shimfidar bututun iskar gas, don haka lokacin da muke son siyan Arsenal shine a shekarar 2020" inji shi.

Mai kamfanin Dangote Group ya kara da cewa zasu fara magana da wadansu dake son su siyar da kason su a kungiyar.

Advertisement

Ya kara jaddada cewa a gaskiya ba yin haka shine muhimmin abun dake gaban su a halin yanzu.

Advertisement
Latest Videos
Advertisement