Tauraruwar Kannywood, Hadiza Aliyu Gabon ta girgiza zukatan maza da sabbin hotuna da ta wallafa a shafin ta.
Jarumar dandalin fina-finan hausa ta wallafa hotunan a shafin ta na Instagram wanda ya dauke hankalin masoyan ta da masu bibiyan shafin ta.
Daga ganin hotunan da irin fara'ar da take nuna ana iya cewa jarumar ta kai karshe da wadanda take bin bashin kudi.
Hadiza Gabon da wadanda take bin bashi
Ga wadanda basu sani ba, a kwannan baya ne Hadiza Gabon tayi barazanar wallafa sunayen wadanda take bin bashi matukar basu yi gaggawar biyan ta ba.
A sakonnin da ta wallafa a shafin ta, jarumar shirin "Indo" ta nuna bacin ran ta ga abokan mu'amalar ta da take neman su biya ta bashin da suka ara.
kamar yadda ta sanar, ciki akwai kudin aikin da tayi ba gama biyanta da kuma kasuwanci da tayi shima ba'a biya ta kudin ta ba.
Da yawa daga cikin masu bibiyan ta kafafen sada zumunta sun goyi bayan matakin da ta dauka kuma sun koka kan yadda mutane ke cin bashi ba tare da nuna alamar biya.