Advertisement

Gwamnan jihar Niger ya yanke alaka da wadanda ke mai yakin neman zaben 2019

Governor of Niger State, Abubakar Bello.
Governor of Niger State, Abubakar Bello.
Gwaman Abubakar Bello ya yanke alaka da magoya bayan shi dake lika postan neman zaben 2019.
Advertisement

Kwamishnar labarai na jihar Mr Jonathan Vasta ya bayyana ma manema labarai haka ranar laraba a garin minna.

Advertisement

“Gwamnan da gwamnatin jihar Niger bata da alaka da wadanda wannan wahalar, don baya daga cikin dabi’un gwamnatin mu”

“Gwamnan ya yarda da dokar kasa kuma baya goyon bayan duk wanda ke kamfe indai hukumar zabe na kasa bata bada umarni na yin haka ba”

Vasta yace Bello baya bukatar ire-iren wanan aiki su shagaltar dashi a wannan lokaci da yake neman cika alkawullan da ya dauka lokacin kamfe.

Ya kara da cewa gwamnan na aiki da tsarin dokar kasa kamar yanda tsarin demokradiya ke bukata.

Advertisement

Kwamishnan yace wata kila aikin masu neman barna.

Yayi kira ga jama’a da suyi watsi da labarin neman zaben 2019.

Advertisement
Latest Videos
Advertisement