Advertisement

Matar dan wasan super eagles ta karyata labarin dake yaduwa na cewa mijinta ya lakada mata duka

A labarin da ya fito ranar lahadi, ana zargin dan wasan da raunata uwardakin sa bayan rashin jituwa da suka samu a gidan su dake nan jihar Sakkwato.
Advertisement

Matar jajirtaccen dan wasan kwallon tawagar super eagles ta Nijeriya ta karyata labari dake yaduwa na cewa mijinta Abdullahi Shehu ya lakada mata duka.

Advertisement

A labarin da shahararren kafar watsa labarai Instablog ta fitar, an zargin mai tsaron bayan tawagar nijeriya daga hannu ma matar sa bayan rashin jituwa da suka samu bisa ga kin amsa kiran waya.

Kamar yadda labarin ya fito, lamarin ya faru ne a nan gidan su dake jihar Sakkwato ranar lahadi 15 ga wata.

Labarin ya mamaye kafafen sada zumunta inda ya zamanto batun muhawara a dandalin. Jama'a da dama sun nuna bacin ran su ga lamari tare da yin Allah-wadai ga mazaje masu dukar matan su.

Advertisement

Sumayya Mustapha ta karyata labari

Sai uwardakin dan kwallon ta karyata wannan labarin ranar litinin 16 ga watan Yuli.

A labarin da mujallar Tozali ta fitar, Summaya tace babu abun da ya faru tsakaninta da mijinta kuma labarin dake yaduwa na cewa tasha duka a hannun maigidanta ba gaskiya bane.

Uwardakin Sumayya Mustapha ta yaba so da kauna da suke da dan kwallon tare da jinjina masa bisa kulawarn da yakje nuna mata.

Dangane da hoton rauni da ta samu a ido, tace lamarin ya faru ne tun kwanakin baya kuma ta same shi ne sakamakon hatsari da ta samu.

Advertisement

Daga karshe ta kira lamari da jarawaba daga Allah domin a cikin duk wata falalar da mutum ya samu akwai jarabawa dake tare da ita.

Advertisement
Latest Videos
Advertisement