Wasu yan bindiga sunyi garkuwa da mai kula da harkar kasuwanci na hukumar NHIS
An samu labari cewa wasu yan bindiga sunyi garkuwa da mai kula da harkar kasuwanci na hukumar inshorar kiwon lafiya NHIS Zakari Muhammed Sada.
Rahoto ya bayyana cewa Sada na hanyar tafiya zuwa kaduna daga Abuja lokacin da yan bindigar suka tare motar shi a babban hanya kusa da garin Katari.
Yan tawayen sun shiga daji da shi inda suka nemi iyalin shi da su biya kudin fansar shi.
Ba’a samu labarin yawan kudin da yan garkuwan suka bukaji iyalin sa su biya lokacin da aka yi wannan rahoto.
Rundunar yan sanda na jihar basu samu sun tabbatar da lamarin lokacin da ake tunanin ya faru.
Wannan lamarin ya faru bayan wasu yan bindiga da ake tunanin yan garkuwa da mutum ne suka kai hari ma matafiya ranar juma’a 7 ga watan Yuli a babban hanya sashen garin Katari inda ma suka kashe wata mace.