Mummunar musayar wuta tsakanin wasu sojoji da ‘yan sanda a garin Aba na jihar Abia ta yi sanadiyar mutuwar ‘yan sanda biyu da soja daya tare da raunata mutane da dama.
Mummunar lamarin ya faru ne a ranar Juma’ar 15 ga watan Yuni.
Kwamishanan yada labaran jihar, Cif John Okiyikalu, ya sanar cewa da jin aukuwar lamarin gwamnatin jihar ta yi maza maza ta taro shugabannin sojoji da ‘yan sanda domin ganawar gaggawa da zummar yayyafawa rikicin ruwan sanyi.
A rahoton da VOA ta fitar, gwamnan jihar Abia ya kafa kwamitin bincike domin gano musabbabin rikicin tare da sanin matakin da za’a dauka na hana sake aukuwar lamarin. Jihar tana son ta tabbatar jami’an tsaron suna aiki tare cikin kwanciyar hankali da lumana.
Wani tsohon soja mai ritaya dake sharhi akan harkokin tsaro ya yi tsokaci yana mai cewa “Sojoji suna da nasu aikin da tsarin mulki ya tsara masu, na kare mutuncin kasa yayinda aikin ‘yan sanda ne su inganta matakan tsaron cikin gida. Amma idan aka hada sojoji da ‘yan sanda su yi aiki tare dole a samu matsala saboda haka wajibi ne gwamnati da dinga waresu”.
Tsohon sojan yace bai kamata ana tura sojoji su yi aikin da ‘yan sanda ke yi ba.