ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Tauraruwar Kannywood ta samu kyautar Jarumar jarumai na shekara

A bikin karrama fitattun yan Njieriya da suka taka rawar gani wajen cigaban kasar da aka gudanar a garin Abuja daren ranar alhamis 24 ga watan Mayu ta samu kyautar.

Kasancewar tana kasar Cyprus inda take karatu, tauraruwar masana'antar kannywood ta samu wakilcin jarumi Uzee Usman wanda ya amshi kyautar a madadin ta.

kamar yadda ta wallafa a shafin ta tare da hoton lambar yabon, Rahama Sadau ta nuna farin cikin ta da samun kyautar bayan an hada ta gasa da wasu fitattun jarumai.

Tayi ma dinbim masoyan ta godiya bisa goyon bayan da suke bata na yau da kullum wanda dashi take takama.

ADVERTISEMENT

Daga karshe tayi ma jaridar Leadership godiya ta karramawar da suka bata tare da Uzee wanda ya amshi kyuatar a madadin ta.

Jaruma ta samu kyauta ta musamman a kasar Amurka

Wannan shine kyauta na biyu da jarumar ta samu bana.

A cikin watan Maris, jarumar ta samu lambar yabo ta musamman a taron bikin fina-finai da aka shirya a birnin New york dake kasar amurka.

Gidauniyar Global Women Empowerment network wanda ke karkashin kulawar majalisar dinkin duniya ta karrama ta da lambar yabo bisa rawar da take taka wa wajen daga tutar mata.

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT