ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Buhari yayi ma yan APC da suka sauya sheka fatan alheri

Shugaban ya kara da cewa gwiwar ya'yan jam'iyar ya fara yin sanyi, a cewar shi ana yawan samun haka da zaran lokacin zabe yayi kusa.

Yan majalisar dattawa 15 suka fice daga jam'iya mai mulki yayin da yan majalisar wakilai 37 suma suka yi balaguro dag jam'iyar APC.

A cikin wata takarda da hadimin sa Garba Shehu ya fitar, shugaba Buhari ya bukaci sauran yan'yan jam'iya da kada su karaya ga faruwar hakan.

Yace uwar jam'iyar tayi kokarin hana su sauya sheka amma hakan bata samu ba. A bayanin sa shugaban yace jagoran APC yana kokarinsa sa ba dare ba rana domin hada kan yan jam'iyar.

ADVERTISEMENT

Yace babu wani daga cikin yan majalisar da suka sauya sheka da yake da matsalar da gwamnatin sa kuma shima wani daga cikin su da yake da matsala dashi. Yace yana mutunta yancin su na zabar ko wani jam'iya da suke da ra'ayin shiga kamar yadda tsarin doka ya tanadar.

Daga karshe shugaban yace a shirye yake yayi aiki da majalisar dokoki tare da membobinta ba tare da la'akari da bambamcin jam'iyar su.

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT