Pulse.ng logo
Go

Damfara Kamar yadda aka yi ma takawaranta, Hadiza Gabon tayi jan hankali

Ta nisantar da kanta da shafin tare da yin kira ga jama'a da su kaurace ire-iren shafukan bogi masu bukatar kudi daga masu bibiyan ta.

  • Published:
Hadiza Gabon play

Hadiza Gabon

(Instagram)

Shaharariyar jarumar fim Hadiza Aliyu Gabon tayi jan hankali ga masu bibiyan ta a kafafen sada zumunta da suyi hattara da masu bude shafukan bogi da sunan ta.

Jarumar ta haska wani shafin bogi da aka bude da sunan ta wanda ke rokon jama'a da su tallafa da kudi domin tallafawa mara hali.

Ta nisantar da kanta da shafin tare da yin kira ga jama'a da su kaurace ire-iren shafukan bogi masu bukatar kudi daga masu bibiyan ta.

wannan yana daya daga cikin abubuwa dake ci ma jaruman kannywood tuwa a kwarya shine yawan bude shafukan bogi da sunan su tare da neman kudi daga jama'a ta hanyar da wasu bata gari keyi.

Tauraruwar kannywood tana mai cewa "Wallahi wannan ba ni bace ba pls beware and pls repost#beware#fraud #fakeaccount"kamar yadda ta rubuta a shafin ta na instagram tare da hoton shafin bogi wanda aka bude da sunan ta a facebook.

Lamarin Maryam Booth

Lamarin nata yayi kama da na takwaranta Maryam Booth wanda ta nuna bacin ran ta ga masu fada ma yan damfara masu amfani da sunayen jarumai wajen damfara.

A sakon da ta wallafa a shafin ta tare da bayyana hoton shafin da aka bude da sunan ta, jarumar tayi kira ga jama'a da su sani cewa ita bata taba neman bukatar kudi daga masoyan ta domin sanin kowa ne cewa ita tana gudanar da harkar kasuwanci.

Tayi fashin baki inda ta zagi masu aikata ire-iren harkar damfara kuma ta jingina bakar ta albakarcin wannan watan Ramadan da ake ciki.

 

Do you ever witness news or have a story that should be featured on Pulse Nigeria?
Submit your stories, pictures and videos to us now via WhatsApp: +2349055172167, Social Media @pulsenigeria247: #PulseEyewitness & DM or Email: eyewitness@pulse.ng. More information here.