ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Maryam Booth ta nuna bacin ran ta ga masu amfani da sunan ta wajen yin damfara

Daya daga cikin abubuwa dake ci ma jaruman kannywood tuwa a kwarya shine yawan bude shafukan bogi da sunan su tare da neman kudi daga jama'a ta hanyar da wasu bata gari keyi.

Maryam ta nuna bacin ran ta ga masu damfara wadanda suke amfani da sunan ta wajen karbar kudin jama'a.

Ban da haka jaruman suna kara fuskanta barazanar daga masu satar bayanar sirri ta hanyar konfuta.

A hallin yanzu dai jaruman sun tsaurar matakin kan wadanan matsaloli da suke fuskanta kuma Maryam ta gano matakin da suke bi wajen yin damfara.

ADVERTISEMENT

A sakon da ta wallafa a shafin ta tare da bayyana hoton shafin da aka bude da sunan ta, jarumar tayi kira ga jama'a da su sani cewa ita bata taba neman bukatar kudi daga masoyan ta domin sanin kowa ne cewa ita tana gudanar da harkar kasuwanci.

Tayi fashin baki inda ta zagi masu aikata ire-iren harkar damfara kuma ta jingina bakar ta albakarcin wannan watan Ramadan da ake ciki.

Tana mai cewa duk wanda aka kama mai aikata wannan laifin ya sani cewa ba za'a takaita matakin hukunci ba.

Daga karshe tayi Allah-wadai ga masu baiwa mutane kudi ba tare da sun tabbatar da sahihancin wanda ke neman bukatar. "Sai kace wanda ke da tabin hankali"? ta mai bayana cewa ita dai bata taba nemi bukatar masoyan ta ba alhali tana kasuwanci.

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT