A yau ne shugaban majlisar dattawa, Bukola Saraki, zai san matsayin shi bisa barazanar tsige da wasu yan majalisar APC keyi.

Yan majalisar zasu koma zama yau Talata 9 ga watan Oktoba bayan shafe kusan wata biyu suna hutu.

Majalisar ta tafi hutu ne bayan lamarin da ya faru a gidan shugaban majalisar inda wasu jami'an tsaro suka tare hanyar shiga da fita gidan shi dake nan babban birnin tarayya.

Jim kadan bayan faruwar lamarin, Bukola Saraki,ya sauya sheka daga jam'iya mai mulki ta APC zuwa tsohon jam'iyar shi taPDP bayan da ya zargi jam'iyar da yi masa bita da kulli wanda ya saba wa tsarin dimokradiya.

Sai dai wannan matakin da ya dauka ya tada kura a jam'iyar APC inda yan majalisun jam'iyar suka sha alwashin tsige shi daga matsayin shi.

Tun a lokacin da majalisar take hutu, jam'iyar take kira na a dawo zama domin amince da kasafin kudin gudanar da zaben 2019 da shugaba Muhammadu Buhari ya mika ma zauren. Sai dai wasu na ganin cewa hakan wani makarkashiya ce na kaddamar da anniyar tsige shugaban majalisar.

Shima shugaban jam'iyar APC na kasa, Adams Oshiomole, ya sha bayyana cewa shugaban majalisar zai sauka daga mukamin sa ta hanyar da dimokradiya ta tanadar muddin bai sauka da kansa ba.

A farko dai majalisar ta sa ranar 26 ga watan Satumba a matsayin ranar dawowa da zama sai dai g=daga baya ta daga domin baiwa jam'iyu gudanar da zabukan fidda gwani.

Shima kakakin majalisar wakilai, Yakubu Dogara, ya fuskantar barazanar da takwaranshi na zauren dattawa ke fuskanta bayan da shima ya sauya sheka zuwa jam'iyar adawa.