ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Kwana daya kafin gasar kofin duniya, tawagar Spain ta sallami kocin ta

An sallame shi bisa ga amincewa ga yarjejeniyar horas da yan wasan Real Madrid bayan kammala gasar duniya ba tare da sanar da hukumar kwallon kasar

Sanarwan ya zo kwana  gabanin fara gasar cin kofin duniya kuma kwana biyu kafin kasar ta kece raini da kasar Portugal.

Kociyar dai ya amshi aikin horas da yan wasan tawagarReal Madrid bayan kammala gasar duniya ranar 12 ga watan yuni a yerjejenya wacce zata sa ya cigaba da horo har tsawon shekara 3.

Kamar yadda shugaban hukumar kwallon kafar Spain,  Luis Rubiales, ya sanar an sallame shi ne bisa amincewa da yayi ga aikin kungiyar Real madrid ba tare da sanar da hukumar ba.

Rubiales ya kara da cewa duk da cewa tawagar yan wasan zasu yi kewar sa, hakan ba zai hanu su mayar da hankali ga wasan su da Portugal.

ADVERTISEMENT

Akwai rahotanni dake yaduwa a kafafen watsa labarai cewa tsohon dan wasan Real Madrid, Fernandes Hierro zai maye gurbin sa.

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT