Advertisement

Sarkin Kano ya jagorancin gwamna da sauran jama'a sallar Idi

Sarkin kano Alhaji Muhammad Sanusi na biyu ya jagoranci sallar idi wanda aka gudanar a babban fili dake kofar mata
Advertisement

Sarkin ya sanar cewa an gano jinjirin watan ne a yankuna a jihar Kano, Kaduna, Sakwato da Borno da sauransu.

Advertisement

A jihar Kano Sarki, Alhaji Muhammad Sanusi Na biyu, ya jagorancin al'ummar sa wajen yin sallar Idi ciki har da gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje da sauran ma'aikatan gwamnatin jihar.

Manyan yan majalisar sarkin kano suma sun halarci sallar idi wanda aka gabatar a babban filin idi dake nan kofar mata.

Shima sarkin garin Iwo dake jihar Osun, Oba Abdulrasheed Akanbi, ya halarci sallar idi tare da al'ummar jihar Kano.

Advertisement
Latest Videos
Advertisement