Advertisement

Shahararren malamin addini ya rasu

Tsohon shugaban kungiyar limamai na jihar Kaduna ya rasu a yammacin ranar litinin 10 ga watan Satumba.
Advertisement

Shahararren malamin addinin musulunci Sheikh Usman Babatuni Zaria ya rasu bayan rashin lafiya da ya sha fama da ita.

Advertisement

Marigayin shine limamin masallacin NNPC na Kaduna kuma ya rasu a asibitin koyo ta jami'ar Ahmadu Bello dake Shika inda yake jinyar ciwon suga.

Tuni aka yi jana'izatr sa a garin Zaria kana a binne shi a makabartar Dambo dake nan Zazzau.

Ya rasu yana da shekaru 75 a duniya kana ya bara mata biyu da yara 21.

Advertisement
Latest Videos
Advertisement