Gwarzon dan wasan kungiyar Liverpool da tawagar yan wasan kasar Senegal Sadio Mane ya mamaye shafuka a dandalin sada zumunta bisa ga wannan bidiyon inda yake taimakawa wajen wanke bahaya da wurin alwala na masallacin.
Masallacin mai suna Al-rahman dake nan titin Mulgrave a birnin Liverpool na kasar Ingila nan ne dan wasan yake gabatar da sallolin sa.
Wasan da Liverpool tayi da kungiyar Leicester wanda aka tashi 2-1, dan kasar Senegal ya zura kwallo daya a raga wanda ya taimaki kungiyar sa wajen samun galaba a kan abokan adawar su.
An haifi Mane ne a cikin addinin musulunci, kuma ya girma a garin Bambali dake kudancin kasar Senegal inda mahaifinsa ne limamin masallacin garin, hakan ya sanya shi mutumi mai riko da addini.
Dan wasan mai shekaru 26 a duniya yana daya daga cikin fitattun yan wasan kwallon kafa dake alfahari da addinin su. Yakan yi sujududa don nuna godiya idan yayi nasarar zura kwallo a raga.
Dan kwallo yana daya daga cikin yan wasa da ake jin duriyar su a duniyar kwallon kafa ta duniya a halin yanzu.
Yayi nasara lashe gwarzon dan wasan watan Agusta ta gasar firemiya sakamakon rawar da ya taka ma Liverpool a watan.