Advertisement

Hotunan jaruma tare da mahaifiyar ta a kasa mai tsarki

Tauraruwar tare da mahaifiyar ta suna cikin mahajjata da suka gudanar da aikin hajj bana.
Advertisement

Hakika daya daga ciki abun farin ciki da mutum yake alfahari dashi shine kasancewa tare da iyaye musamman mahaifiya, Rahama Sadau bata boye soyayyar da take ma mahaifiyar ta.

Advertisement

Fitacciyar jarumar ta sha nuna ma masoyan ta da ma'abotan shafin ta na dandalin sada zumunta cewa ita da iyalen gidan ta babu shamaki ga soyayyar dake tsakanin su duba da irin kirari da take masu tare da saka hotunan su akai-a-kai.

A cikin hotunan da jarumar ta wallafa a shafin ta na Instagram an gan inda take wasa da dariya tare da mahaifiyar ta a harabar masallacin Saudiya.

Rahama Sadau ta fito takarar gasar AMAA

Bana dai jarumar wacce take safarar basira da kwarewarta a masana'antar Kannywood da Nollywood tana cikin jaruman Afrika da suka fito takarar gasar AMMA.

Advertisement

AMAA awards gasa ne wanda ake karrama fitattun yan wasan kwaikwayo da suka taka rawar gani a masana'antar fim na ko wace kasa dake nahiyar Afrika.

Jarumar zata fafata da fitattun jarumai wajen lashe lamban yabo ta "best Actress in supporting role" wato jaruma mafi birgewa a bangaren mai mara wa jarumi baya a fim.

Ta shiga cikin ya takarar ne bisa rawar da ta taka a cikin shirin "Hakkunde".

Banda ita, shirin fim da jarumi Ali Nuhu ya shirya wato "Mansoor" ta fito takara a gasar a rukunin shiri mai dauke da labari cikin harshen gargajiya.

Bikin gasar na wannan shekarar zata kaya a Kigali babban birnin kasar Rwanda ranar 22 na watan Satumba.

Advertisement
Advertisement
Latest Videos
Advertisement