An koma kama jaruma da ta tsere daga kurkuku shekara shida da ya gabata bayan hunkuncin kisa
Jaruma Rabi Ismail da aka yanka wa hukuncin ratayewa saboda kisan kai ta tsere daga kurkuku a Haɗejia, Jihar Jigawa inda take jiran hunkuncin.
Sashin leƙen asiri na Kurkukun Najeriya, tare da goyon bayan ƴan Mazan aikin tsaro na jiha, SSS sun koma kama Allah wadai Jarumar fim na Hausa Rabi Ismail, da ta tsere daga kurkukun Haɗejia a disamba 16, 2011.
An yanka wa Rabi Ismail kisa ta hanyar rataya domin aikata kisan kai daga wani babban kotu a Kano a ranar 5 na Janairu, 2005.
A watan Yuli na Shekara 2011, Kotun Koli ya amince Hukunci na ƙananan Kotu da ta yanka mata hukuncin kisa ta hanyar rataya domin kisan Abokin ta, Auwalu Ibrahim domin samun dukiyarsa. Kotun ta same ta da laifin guba da kuma Nutsar da Ibrahim a 2002, a Kano.
Controller Janaral na Gidajen yari ya nuna godiya saboda taimako daga hukumomin tsaro musamman SSS da ƴan sanda a kama ta.
Ya yi kira ga jama'a su ci gaba da samar da bayanai masu amfani a kan masu gudu daga gidan yari, da kuma duk mai laifi a tsakiyarsu zuwa ga Jami'an tsaro, Abin lura irin wadannan mutanen na a matsayin barazanar tsaro ga al'umma.
Ya tabbatar da cewa an ƙarfafa matakin tsaro domin hana mutane a gidan yari tserewa.