Advertisement

Matasa masu yi ma kasa hidima 1,596 cikin 2,126 sun bukaci a canza masu jiha a Adamawa

Jami'in dake kula da shirin NYSC a jihar Adamawa yace mafi yawancin matasan da aka turo jihar sun nemi a canza masu jiha
Advertisement

Cikin su 2,126 da aka turo jihar, mutum 1596 sun nemi a tura su wata jiha banda jihar Adamawa.

Advertisement

Jami'in dake kula da shirin NYSC a jihar Adamawa, Mallam Abubakar, yace mafi yawancin matasan da aka turo jihar sun nemi a canza masu jiha.

Ya kara da cewa, yayin da aka mika ma matasan takarda  bayan horo da aka gudanar ma sabbin shiga shirin, mafi yawanci sun ki amincewa da inda aka tura su domin cigaba da aikin bautar kasa.

Kamar yadda ya sanar, matasan sunki amincewa da cigaba da bautar bisa ga dalilin matsalar tsaro da rashin lafiya da dalilin rayuwar aure.

Sauran matasa 530 da suka amince da cigaba da yin hidima a jihar, Malam Abubakar ya sanar cewa ba'a tura su kananan hukumomi na jihar irin su Michika da Madagali da Mubi da kudu da mubi ta arewa, bisa ga dalilin matsalar tsaro da suke fuskanta.

Advertisement

Yayi kira ga jama'ar jihar da su mara ma matasan da suka amince da yin aiki a jihar baya wajen tafiyar da aikin su yadda ya kamata.

Advertisement
Latest Videos
Advertisement