Wata Mace ta watsa ma mijinta mai wande yake da zafi a ranar Kirismeti
Wata ƴar ƙasar Kenya mai suna Evelyn Atieno, ta yi bayanin dalilin da ya sa ta watsa ma Maigidanta-Bruce Omondi-zafin mai a ranar Kirismeti.
Wannan mata tana da zama a ƙauyen Likoni, a Jihar Mombasa, cikin ƙasar Kenya. Ta zargi mijinta da alfasha, sai ta saye kwalban mai na girki. Bayan ta tabbatar da zafin mai, sai Evelyn ta watsa mai a jikin mijinta.
Ƴan gidan jaridan Daily Post, sun yi rahoto cêwa Evelyn ta tsere daga masaukinsu bayan ta aukar da wannan laifi. A yayin da sauran mutane suna fama da nishaɗi na bikin kirismeti, Mr Omondi, maigidan Evelyn, ya ci gaba da wahala a asibiti na ƙauyen Likoni domin yanayin jikinsa wanda ya ƙone sossai. Daga baya, an garzaya da shi zuwa babban asibiti domin cikakken kula.
Yan sanda sun kama wannan mata. Tana da shekara 30. Ana shirye-shirye domin hukuntar da ita a cikin lokaci. Sufiritanda mai kula da offishin yan sanda,Willy Simba, ya tabbatar da wannan labari wanda ya faru a rnar 30 ga watan Disamba. Ya bayyana cewa akwai alamar jayayya da rashin fahimtar juna tsakaninsu. Ya kara bayani cewa, ya kaddamar da bincika na kamun mai laifi a ranar Juma'a.
Bugu da ƙari, Omondi ya bayyana cêwa matansa ta nuna masa mugun halaye. Ya bayar da labarai game da azbtar da tashin hankali wanda yake fama da shi tun shekara ukku bayan aurensu.