Advertisement

'Yan Biyu sun sake saduwa bayan an raba su a lokacin haihuwa

'Yan Biyu sun sake saduwa bayan an raba su a lokacin haihuwa
'Yan Biyu sun sake saduwa bayan an raba su a lokacin haihuwa
Wasu tagwaye (waton 'Yanbiyu') sun sake saduwa akan shirin gidan talabijin bayan sun rabu a lokacin haihuwa.
Advertisement

Wasu tagwaye sun sake haɗuwa akan shirin "Ina kwana ʼƴan ƙasar Amirka" na gidan talabijin ABC News, bayan an raba su a lokacin haihuwa.

Advertisement

Yaran suna da asalinsu a ƙasar China. A shekara goma na baya, wasu iyalai biyu daban-daban daga Amirka sun tallafa iyayen waɗanan yara a yayin da sun ɗauke su zuwa Amirka. Bayan shekara goma, gidan talabijin na ABC sun haɗa shirn  wanda ya sake tara su a wuri guda.

A lokacin da suka haɗu, waɗannan yanbiyu masu kamá sossai sun yi hawaye, kuma sun rungumi juna. Wannan shi ne farkon saduwansu. Yarinya na farko-mai suna Audrey Doering- tana zama a garin Wisconsin. Yarinya na biyu mai suna Gracie Rainsberry, tana zama a garin Washington State.

Audrey ta faɗa ma Ƴan gidan talabijin na ABC News cêwa ta daɗe tana neman saduwa da iyayenta, har dai a lokacin kirsimeti. Amma ba ta san cêwa wasu iyalai daban sun ɗauki ƴar uwanta zuwa Amirka ba. Ƴan gidan talabijin na ABC News sun haɗa wannan saduwa ba tare da sun sanar da waɗannan yara cêwa tagwaye ne.

Bayan ta haɗu da ʼyar uwanta, Gracie ta yi bayani haka:

Advertisement

"Ina farin-ciki sossai, kuma ina ji saran saboda wannan saduwa."

Yar uwata Audrey ta amsa cewa:

"Kullum ina lura da cêwa rayuwana bai cika ba, kamar wani abu ya ɓâtta daga jiki na. Yau na samu abinda ya bâtta, kuma komi ya yi daidai yanzu."

Audrey ta ƙara bayani cewa:

"A lokacin da aka faɗa min cewa ina da ƴar uwa wanda aka haife mu a lokaci guda, na yi tsamani cêwa ana yi min zazzaga ko wargi ne kawai. Amma bayan na sadu da ƴar uwata, na yi mamaki da ganin mutum mai daidai kama da ni."

Advertisement

Duka Æ´an biyu sun yi hawaye sossai a lokacin da suka sadu.

Abin mamaki shi ne, duk da rashin saduwarsu, waɗannan yan-biyu suna da raʼayi da halaye mai kama sossai. Misali; Kowanensu na da raʼayi na cin cuku da naman kaza. Bugu da ƙari, waɗannan ƴan-biyu suna fama da ciwon zuciya. Audrey ta shiga tiyata so biyu, Gracie ta shiga tiyata so guda.

Duk da rabuwan da aka yi musu, an samu damar gane wurin zaman kowanensu a yayin da iyalin da suka ɗauki renón Gracie sun lura da zanen jarfa na hoton yarinya mai kama da Gracie a jikin Mai renón Audrey. Sai ta bincika akan facebook. Daga baya, iyayen da suka ɗauki waɗanan yara reno a Amirka sun shirya sauwarsu tare da Gidan Talabijin na ABC News.

Wannan labari ya ba mutane mamaki sossai. Sun yi murna cêwa yaran da aka haifa a Ƙasar China, sun sadu a Ƙasar Amirka bayan iyaye daban-daban sun ɗauke su reno.

Advertisement
Latest Videos
Advertisement