Advertisement

CAF ta dakatar da lafarin Nijeriya kan laifin cuwa-cuwa

Mai laifin, Joseph Ogabor ya samu wannan mataki bisa lafin da yayi na kokarin karkatar da wasa
Advertisement

Mai laifin, Joseph Ogabor ya samu wannan mataki bisa lafin da yayi na kokarin karkatar da wasa.

Advertisement

Kamar yadda CAF ta sanar,  lamarin ya faru ne a wasan da aka buga tsakanin kulob din Plateau United na Najeriya da USM Alger na Aljeriya a gasar cin kofin zakarun Afirka na Confederation Cup ranar 7 ga watan Afrilu a Legas.

Matakin ya biyo bayan bincike da kuma shaidun da jami'an da suka kula da wasan da Afirka ta Kudu suka gabatar, wadanda Ogabor ya tuntuba domin neman su tallafawa kulob din na Najeriya,.

An kuma gargadi Plateau United "da su daina bai wa jami'an wasa kyaututtuka wadanda akan iya yi wa kallon wani yunkuri na cin hanci."

Hukumar dai ta dakatar dashi na tsawon shekara daya.

Advertisement
Latest Videos
Advertisement