Bisa ga rahotannin lamarin ya faru ne a daren ranar talata a gonar dake kauyen Karshi dake wajen garin babban birnin tarayya.
A kwanan baya ne shugaban EFCC ya gama gina gidan da zai zauna a cikin harabar gonar amma bai kai ga tarewa.
Wannan shine karo na biyu da yan bindiga zasu kai hari ga jamÃ'in hukumar EFCC. A wancan karon sun kai harin ne dai dai ofishin hukumar dake nan Wuse a garin Abuja tare da yin harbe-harbe kana suka aje wata wasika mai dauke da barazanar kashe wani jami'in hukumar mai suna Ishaku Sharu.
Karanta labari shugaban ke cewa>>Da taimakon majiya mun gano naira biliyan 29
Shi dai Ibrahim Magu a halin yanzu yana fama da wadanda ake zargi da yi wa tattalin arzikin zagon kasa bisa ga rawan da yake taka wa wajen ganin an hukunta su.