Dubi Hotunan Shugaba a komawar sa Zuwa London
Shugaba Muhammadu Buhari ya koma London don jinya saboda rashin lafiya da ba a fallasa ba.
Buhari ya bar Najeriya a ranar Lahadi, Mayu 7, bayan taro da Mataimakin sa, Yemi Osibanjo, da shugabannin majalisar dokoki, Bukola Saraki da Yakubu Dogara.
Shugaba ya tashi bayan sanarwar tafiyar sa daga kakakin sa, Femi Adesina.
"Shugaba Muhammadu Buhari zai ci gaba da tafiyar sa zuwa London yau saboda Neman shawara game da jinya daga likitocin sa," Adesina ya ce a wani sanarwa.
“Ya Shirya tashi ranar lahadi da rana, amman ya yanke shawarar ya ɗan jira, saboda shigowar ƴan matan Chibok 82 da suka iso Abuja a baya da rana.”
“Shugaba ya na son tabbatar wa ƴan Najeriya cewa, babu wani dalilin damuwa. yana godiya sosai saboda Adu'a da kuma Fatan Alkhairi daga mutane, kuma ya na fatan za su cigaba da adu'a domin zaman lafiya da haɗin kan Al'umma," ya ƙara cewa.
Adesina ya ƙara cewa, tsawon zaman duba lafiyar Buhari likitocin sa za su yanke shawara a London.
Lafiyar Shugaba ya zama darasin maganar ƙasa da ƙasa tun da ya je hutun duba lafiyarsa a janairu.
Buhari a ƙarshe ya yi kwana 49 a ƙasar waje, kuma da ya dawo ya ce bai taɓa irin wannan rashin lafiyar a duk rayuwarsa ba.Shugaba Muhammadu Buhari ya koma London don jinya saboda rashin lafiya da ba a fallasa ba.
Buhari ya bar Najeriya a ranar Lahadi, Mayu 7, bayan taro da Mataimakin sa, Yemi Osibanjo, da shugabannin majalisar dokoki, Bukola Saraki da Yakubu Dogara.
Shugaba ya tashi bayan sanarwar tafiyar sa daga kakakin sa, Femi Adesina.
"Shugaba Muhammadu Buhari zai ci gaba da tafiyar sa zuwa London yau saboda Neman shawara game da jinya daga likitocin sa," Adesina ya ce a wani sanarwa.
“Ya Shirya tashi ranar lahadi da rana, amman ya yanke shawarar ya ɗan jira, saboda shigowar ƴan matan Chibok 82 da suka iso Abuja a baya da rana.”
“Shugaba ya na son tabbatar wa ƴan Najeriya cewa, babu wani dalilin damuwa. yana godiya sosai saboda Adu'a da kuma Fatan Alkhairi daga mutane, kuma ya na fatan za su cigaba da adu'a domin zaman lafiya da haɗin kan Al'umma," ya ƙara cewa.
Adesina ya ƙara cewa, tsawon zaman duba lafiyar Buhari likitocin sa za su yanke shawara a London.
Lafiyar Shugaba ya zama darasin maganar ƙasa da ƙasa tun da ya je hutun duba lafiyarsa a janairu.
Buhari a ƙarshe ya yi kwana 49 a ƙasar waje, kuma da ya dawo ya ce bai taɓa irin wannan rashin lafiyar a duk rayuwarsa ba.