An yi rajista ná mutane tamanin wajen shiri a jihar Jigawa
Ƙaramin Hukumar Gwaram, sun yi sanarwa cêwa mutane tamanin sun yi rajista domin su shiga auren taro wanda gwamnatin jihar sun tallafa.
Hukumar ʼYan Jaridan Najeriya (NAN) sun cê wannan sanarwa ya fito daga bakin Nasiru Yusif, jamiʼin Labarai na ƙaramin hukuma a ranar 15 ga watan Nuwamba, a birnin Dutse.
Hukumar ʼyan Jaridan Najeriya (NAN) sun yi rahoto cêwa ʼƴan kwamitin zasu ziyarce Maigari domin neman goyon bayansa ga ilmantár da jamaʼá akan amfanin wannan shiri. Yusif ya ƙara bayani cêwa shugaban majalisa, Ilu Shuwarin, ya yi alʼƙawari na bada goyon bayansa game da zama rundunar wannan aure na taro da kuma tabbatar da cêwa an gama lafiya.
Da ma can, Hukumar ʼyan Jaridan Najeriya (NAN) sun yi rahoto cêwa gwamnatin jihar Jigawa sun haɗa kwamitin mai mambobi goma sha tara, domin haddin auren taro saboda amfanin gwauraye da bazawarai na jihar Jigawa a ranar 16 ga watan Yuli.
Yanda Yisuf ya bayyana, masu neman aure sun ƙunshi namiji arbaʼin da mata arbaʼin. Yusif ya cê shugaban kwamitin masu haɗa wannan biki-Abdullahi Basirka, ya baza yawan mutanen da suka shiga wannan shiri a lokacin da masu ruwa da tsaki sun yi gamuwa a ranár Alhamis 17 ga watan Nuwamba.
Sakataren Gwamnatin Jihar Jigawa, Abdulkadir Fanini, shi ne shugaban wannan shiri. Yanda suka yi bayani, gwamnatin Jihar sun kawo wannan hikima domin rage fitina cikin alʼummah.