Shugabancin Najeriya sun ce ʼƴan matan Chibok zasu yi bikin kirsimeti da iyayensu
Ƴan matan Chibok waɗanda sun tsira daga Boko Haram, za su yi bikin kirsimeti da sabon shekara tare da iyayensu. Wannan sanarwa ya fito daga bakin Malam Garba Shehu, Babban Mataimakin Shugaban Ƙasa akan Labaru.
Shehu ya baza wannan sannarwa akan shafinsa na Facebook. Ya cê Maikata masu tsaron ƙasa a asirce, sun tafi da ʼƴan matan Chibok zuwa wajen iyayensu.
Ya ƙaryata wasu rahotannin da ake bazawa akan yanan-gizo, cêwa an ƙara samun ʼƴancin wasu ʼƴan matan Chibok daga hannun ʼƴan Boko Haram. Ana yada jita-jita cêwa an gano wasu ʼƴan mata a Birnin Yola, kuma ana tsamanin cêwa an sake tsirar da wasu ʼƴan mata. Amma Garba Shehu ya bayyana cêwa waɗanan mata su ne waɗanda aka karɓa daga hannun ʼƴan Boko Haram a cikin watan Oktoba.
Shehu ya bayyana cêwa a cikin asirce, Maʼaikatun tsaro suna cikin tattaunawa akan samun ʼƴancin sauran ʼƴan mata wanda suke hannun ʼƴan Boko Haram har yanzu. Kaman yanda ya bayyana, Malam Garba ya cê Sashen Gwamnati mai Tsaro cikin asiri, suna fata cêwa zasu ci saʼa. Garba ya yi bayani haka:
"Abokaninmu masu yada labari cêwa an ƙara sakin wasu ʼƴan matan Chibok, ba mu yi saʼa ba tukuna."
"Har yanzu, muna cikin shawara. Sashen Gwamnati mai Tsaro cikin asiri suna imani cêwa za mu yi saʼa."
"Yau, ʼƴan hukumar DSS sun isad da ʼƴan matan Chibok ashirin zuwa Birnin Yola, a Jihar Adamawa, domin yin bikin kirsimeti da iyayensu."
"Ba a ƙara tsirar da wasu ʼƴan mata ba. Amma da ikon Allah, za a ʼƴantar da su. Ina gaisuwa: Barkan ku da bikin kirsimeti, jamaʼa."
Hukumar Labarai na Najeriya (NAN) sun tuna da labarin ʼƴan mata 276 wanda ʼƴan Boko Haram suka sace a yayin da sun fashe ɗakunansu cikin makarantan Chibok a shekara na 2104.
A cikin watan Oktoba, Gwamnati ta samu saʼa na ƴantar da su , bayan sun tsawanta wajen tattaunawa da waɗanda suka sace su. Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, ya yi alƙawari na tabbatar da cêwa an karɓi sauran matan da aka sace.