Advertisement

Án ƙwace suturan wata buduruwa kuma an bar ta a tsiraice domin satar Kaza ranar Kirismeti

Án ƙwace suturan wata buduruwa kuma an bar ta a tsiraice domin satar Kaza ranar Kirismeti
Án ƙwace suturan wata buduruwa kuma an bar ta a tsiraice domin satar Kaza ranar Kirismeti
An yi ma wata buduruwa dokar daji wanda ba za a iya zato ba, bayan an zarge ta da satar kaza a ranar Kirsimeti.
Advertisement

Wani mumunar aukuwa mai kunya ya faru a garin Nnewi cikin jihar Anambra. An wulaƙántár da watá buduruwa bayan an zarge ta da sátan Kaza domin yin bikin Kirsimeti.

Advertisement

Wata mai suna Precious Eze, ta rubuta akan shafinta na Facebook cêwa an kama wannan buduruwa a lokacin da ta saci kaza a ranar 24 ga watan Disamba, 2016. A nán take, wasu mutane sun yi tarowa kuma sun yi mata dukan tsiya. Sun ƙwace mata sutura. Bayan haka, sun ɗora wannan kaza ga bayanta da nufin ta yi goyon kaza, kuma sun zagaye gari da ita domin yin farati.

Patience ta ba da labarin haka:

“Menene amfanin yin kwaɗayin abinda ba ka da kuɗin saye? " ( A yi hattara da hoton don Allah)

Wannan aukuwa ya faru a Nnewi cikin Jihar Anambra a ranar 24 ga watan Disamba 2016 a yayin da wata buduruwa ta na buƙatar cin naman kaza a lokacin bikin kirismati. Ta saci wannan kaza domin rashin kuɗi na sayen kaza.

Advertisement

Idan baka da kuɗi na sayen kaza, wajibi ne ka ci kaza a ranar bikin kirismeti? Menene ya hana ku cin kifi? Idan ba ka da ƙarfi na sayen kifi, menene ya hana zuwa ziyara wajen makwabcinka wanda ya yanke kazan kirismeti? Yanzu, hotunan wannan buduruwa ya yaɗu akan yanar gizo!”

A cikin makonin da suka wucê, mutane suna a rude game da irin zaluncin da ake yi ma ƙananan ɓarayi masu sata mai tausayi. Amma abin mamaki shine cêwa, mutanen da sun saci arzikin alʼumma gaba ɗaya, basu samun irin wannan wulaƙanci. Sai dai a ɗaukaka su kaman sarki, kuma a yi musu rawani da manyan mukamai domin tayasu murna akan kayan zamba.

Advertisement
Latest Videos
Advertisement