Advertisement

APC ta kebe kujerar gwamna zuwa ga yankin tsakiya

Hakan ya biyo bayan tattaunawar da masu ruwa da tsaki na jam'iyar suka yi a gidan gwamnatin jihar ranar Laraba.
Advertisement

Shugabancin jamiya mai mulki ta APC reshin jihar Zamfara ta kebe kujerar gwamnan jihar zuwa ga yankin tsakiya ta jihar.

Advertisement

Labarin haka ya biyo bayan tattaunawar da masu da tsaki na jam'iyar suka yi a gidan gwamnatin jihar ranar laraba 5 ga watan Satumba.

Jam'iyyar APC a jihar Zamfara ta cimma matsaya kan cewa dan takararta na kujerar Gwamna zai fito ne daga shiyya ta Tsakiya wanda ya kunshi kananan hukumomin Gusau, Maru, Bungudu da kuma Tsafe.

Shugaban Jam'iyyar Alhaji Lawal Liman ya ce, jam'iyyar ta cimma wannan matsayin ne bayan tattaunawar da suka yi kuam yayi kira ga yayan jam'iyar na jihar da su bada hadin kai domin samun nasarar lashe zaben 2019.

Advertisement
Latest Videos
Advertisement