Advertisement

Dandazon jama'a sun sauya sheka daga APC zuwa PDP, sunyi bikin kona tsinsiya

Anyi bikin tarbar su a garin Zonkwa dake karamar hukumar Zangon kataf ranar litinin 7 ga watan mayu
Advertisement

Dan majalisar wakilai na tarayya mai wakiltar Kagarko da Kachia, Honarable Jagaba Adams ya jagoranci sauran jama'a wajen canza sheka.

Advertisement

Anyi bikin tarbar su a garin Zonkwa dake karamar hukumar Zangon kataf ranar litinin 7 ga watan mayu.

Manya jami'an PDP na kasa baki daya da na jiha sun halarci taron bikin ciki har da tsohon shugaban jam'iyar ta kasa, Sanata Ahmed Makarfi.

A jawabin sa, Sanata Makarfi ya gargadi su da su taimaka wajen tabbatar da manufar jam'iyar a jihar da ma kasar baki daya.

Shima shugaban jam'iya na jihar, Dakta Hassan Hyet yayi maraba da masu sauya sheka. Ya kara da yi ,masu  albishir da samun nasara.

Advertisement

Bayan ga taron bikin tarban su, wadanda suka canza akida sun gudanar da biki kona tsintsiya don nuna alamar barin APC.

Advertisement
Latest Videos
Advertisement