Gwamnatin Nijeriya da ta kasar Faransa sun rattaba hannu ga yarjejeniyar dala miliyan 475 domin bunkasa wasu ayyukan zamani don amfanin jamaa.

Hakan ya faru ne yayin da shugaban Faransa, Emmanuel Macron, ya ziyarci fadan shugaba Muhammadu Buhari sakamakon ziyarar kwana biyu da ya kawo Nijeriya.

Yarjejeniyar zata taimaka wajen bunkasa harkokin sufuri a jihar Legas tare da inganta hanyoyin inganta shuka a jihar Ogun da samad da hanyoyin tafiyar ruwa a jihar Kano.

Ministan kudi, Kemi Adeosun, ta rattaba hannu a takarda a madadin gwamnatin jihohin da yarjejeniyar zata amfana a fadar shugaban kasa ranar talata 3 ga wata.

Gabanin  yarjejeniyar shugabannin sun tattauna kan wasu muhimman batutuwa wanda ya danganci bunkasa harkokin kasuwanci da inganta tsaro.

Macron, ya bayyana cewa gwamnatin sa zata taimaka wajen yaki da ta'adancin yan ta'adar boko haram da ISIS da suka addabi al'ummar kasar da sauran kasashen yammacin nahiyar Afrika.

Daga karshe shugaba Buhari, yayi ma matashin shugaban Farsansa godiya bisa taimako da goyon baya da yake wajen kawar da ta'adanci a kasar da sauran kasashen Afrika.

Bayan ganawar shi da shugaban kasa, Emmanuel Macron ya garzaya jihar Legas inda ya halarci wani taro na musamman na raya al'ada a daidai wajen taro da aka gina don mutunta fitaccen mawaki Marigayi Fela Kuti dake nan jihar Legas.