Shugaban kasar Faransa, Emmanuel Macron, ya bayyana dalilin da yasa ya kai ziyara shingen nishadi ta Fela Anikulapo Kuti dake nan jihar Legas.

Dandalin wanda aka fi sani da "African shrine" ta shahara a matsayin gurin shakatawa ga ma'abotan nishadi da yan yawon bude ido.

Bayan tattaunawar da suka yi da shugaba Muhammadu Buhari, shugaban kasar Faransa ya yada zango jihar Legas domin ziyartar shingen "african shrine".

Kamar yadda rahotannin suka bayyana, shugaban  shine na farko da zai kai ziyara dandalin "Shrine".

Shugaba Emmanuel Macron, ya shaida cewa a cikin shekarar 2004 yayi aiki a ofishin jakadanci  dake nan Legas kuma a lokacin ya kan ziyarci dandalin domin tunawa da al'adar Afrika.

A jawabin sa yayin da yake ganawa da manema labarai, matashin shugaban ya bayyana cewa ya zabi ziyartar warin shakatawar ne domin wuri ne na raya al'adar Afrika.

Yace wuri ne na tarihi kuma a nahiyar turai.

Shugaban ya bayyana cewa a shirye gwamnatin faransa take domin bunkasa harkokin wasannin motsa jiki da raya al'ada tsakanin Faransa da Nijeriya domin samad da ayyukan yi ga matasa.