A jihar Adamawa wasu mata biyu sun jajirce kuma sunyi nasarar samun tikitin jamiyar APC na takarar majalisar dattawa.

SanataBinta Masi wacce take daya tilo daga arewacin Nijeriya dake zauren majalisar dattawa tayi nasarar samun tikitin sake tsayawa takara domin wakiltar al'ummar yankin arewacin jihar Adamawa.

Ta samu tikitin cikin ruwan sanyi bayan rashin samun abokin takara mai neman kujerar.

Ita ma tsohuwar yar majalisar wakilai daga jihar, HajiyaAisha Dahiru, zata nemi zarcewa zuwa zauren majalisar dattawa bayan da ta lashe zaben fidda gwanin da jam'iyar APC tayi.

Yar majalisar wacce aka fi sani da Binani doke maza hudu da suka fito takara da ita wajen zama gwanin APC wacce zata kara a zaben 2019 domin wakiltar jama'ar yankin Adamawa ta tsakiya.

Zata nemi ta maye gurbin mai wakiltar yankin, Sanata Abdul-Azeez Nyako, wanda ya sauya sheka daga APC zuwa jam'iyar ADP kuma wanda ke neman zaman gwamna a zaben 2019 karkashin sabon jam'iyar da ya koma.

Ta samu kuri'u 1, 282 yayin da mai binta a baya, Alhaji Wakili Boya, ya samu kuri'u 599 na kuri'un da aka kada.

Shima dan majalisa mai wakiltar kudancin jihar Adamawa karkashi jam'iya APC, SanataAhmed MoAllayidi, ya samu tikitin tsayawa takara cikin ruwan sanyi.