ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Sakamakon zaben da aka gudanar ranar Asabar

APC ta lashe zabe uku yayin da PDP ta samu daya a zaben maye gurbi da aka gudanar a jihohi hudu ranar asabar.

Ga yadda samakon zaben take:

A jihar Katsina

A zaben takarar dan majalisar dattawa mai wakiltar yankin Daura na jihar, Ahmed Babba-Kaita na jam'iyar APC ya lashe zaben.

ADVERTISEMENT

Ya doke yayarsa Kabir Babba-kaita na jam'iyar PDP inda ya samu kuri'u 224,601 sabanin kuri'u 54.

Tsohon dan majalisar wakilai zai maye gurbin marigayi Mustapha Bukar wanda ya rasu cikin watan Afrilu na bana.

Jihar Bauchi

A zaben maye gurbin dan majalisar dattawa na yankin kudancin jihar Bauchi, Lawal Gumau ya doke tsohon gwamnan jihar Isa Yuguda da sauran yan takara wajen lashe zaben.

Dan takarar APC ya samu kuri'u 119,489 yayin da dan takarar ya zo na biyu da kuri'u 50,256.

ADVERTISEMENT

PDP tayi nasara a karamar hukuma daya na daga cikin bakwai dake mazabar.

Jihar Kogi

Duk da matsalar sace akwatin zabe da aka samu a zaben dan majalisar wakilai na tarayya da aka gudanar a yankin Koton karfe da Lokaja na jihar, hukumar zabe ta sanar cewa dan takarar APC ya lashe zaben.

Haruna Isa na APC ya doke abokin takarar sa na PDP Injiniya Bashiru Abubakar wajen lashe zaben.

Ya samu kuri'u 11,078 yayin da sauran abokan takarar shi suka samu kuri'u kamar haka

ADVERTISEMENT

Accord - 31, ADC - 977, DA - 47, LP - 14, NPN - 10, NCP - 39, PDP - 7,094 sai kuma SDP wanda ta samu kuri'u 433.

Jihar cross river

A zaben cike gurbin dan majalisar dokokin jiha, yar takarar jam'iyar PDP Abbey Ukpukpen ta lashe zaben da kuri'u 12,712 sabanin kuri'u 4,345 da dan takarar APC ya samu.

Zata maye gurbin mijinta wanda ke rike da kujerar gabanin mutuwar sa a cikin watan Mayu.

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT