Kungiyar yan kabilar Ibo na kasa ta Igbo National Council (INC) tayi kira ga shugaban ƙasa Muhammadu Buhari da ya tabbatar ya samu Mataimaki dan kabilar Ibo kafin zaben 2019.
Kungiyar yan kabilar Ibo ta baiwa Shugaba Buhari bukatar su na zaben 2019
Shugaban ƙungiyar yace ya zama dole Buhari ya biya bukatunsu idan har yana son su zabe shi
Kungiyar tace dole Buhari ya biya bukatunsu idan har yana son su zabe shi a zaben 2019.
A bisa labarin da daily post ta fitar shugaban kungiyar Chilos Godsent yace kungiyar tana zargin shugaban kasa da reshin biyan alkawullan da ya dauka ma yan yankin kudu maso gabas.
Dalilin haka?
Wannan ya fito bayan rahotannin sun nuna cewa shugaba Muhammadu Buhari zai ziyarci jihohin kudu nan bada jimawa ba kuma zai fara da jihar Ebonyi.
Masu sharhi na cewa wannan matakin hanya ce ta gina kyakyawar tarayya tsakanin yan yankin da gwamnatin jam'iyar APC.
JOIN OUR PULSE COMMUNITY!
Eyewitness? Submit your stories now via social or:
Email: eyewitness@pulse.ng