Bayan waadin da hukumar zabe ta kasa ta bada na fitar da yan takarar jamiyun dake kasar kafin ranar 7 ga watan Oktoba, ga wasu daga cikin masu neman kujerar shugaban kasa a zaben 2019.

Yan takarar zasu fafata wajen zama jagoran kasar Nijeriya a zaben wanda za'a gudanar nan da wata hudu masu gabatowa.

Jam'iya mai mulki ta APC tuni ta tabbatar da dan takarar ta, hakazalika ita ma babban jam'iyar Adawa ta PDP ta kaddamar da dan takarar ta bayan zabe da taron kasa da ta gudanar a karshen makon da ya shude.

Shugaba Muhammadu Buhari shine wakilin APC yayin da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar yayi nasarar zama dan takarar PDP. Yan takarar sune yan takarar da ake san ran cewa zasu fi samun kuri'u mafi rinjaye a zaben.

Ga dai sunayen yan takarar dake hangar kujerar mulkin Nijeriya kamar haka;

1. Muhammadu Buhari - All Progressives' Congress (APC)

2. Atiku Abubakar - People's Democratic Party

3. Donald Duke - Social Democratic Party (SDP)

4. Kingsley Moghalu - Young Progressive Party (YPP)

5. Obiageli Ezekwesili - Allied Congress Party of Nigeria (ACPN)

6. Fela Durotoye - Alliance for New Nigeria (ANN)

7. Omoyele Sowore - African Action Congress (AAC)

8. Tope Fasua - Abundance Nigeria Renewal Party (ANRP)

9. Eunice Atuejide - National Interest Party (NIP)

10. Olusegun Mimiko - Zenith Labour Party (ZLP)

11. Adesina Fagbenro-Byron - Kowa Party (KP)

12. Ahmed Buhari - Sustainable National Party (SNP)

13. Hamza Al-Mustapha - People's Party of Nigeria (PPN)

14. Alistair Soyode - Yes Electorates Solidarity (YES)

15. Obadiah Mailafia - African Democratic Congress

16. Prince Eniola Ojajuni - Alliance for Democracy (AD)

17. Usman Ibrahim Alhaji - National Rescue Movement (NRM)

18. John Ogbor - All Progressives Grand Alliance (APGA)

19. Gbenga Olawepo-Hashim - Alliance for People's Trust

20. Peter Nwangwu - We the People of Nigeria (WTPN)

21. Edozie Madu - Independent Democrats (ID)

22. Williams Awosola - Democratic People’s Congress (DPC)

23. Habu Aminchi - Peoples Democratic Movement (PDM)

24. Yabagi Sani - Action Democratic Party (ADP)

25. Moses Shipi - All Blending Party (ABP)