ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Aisha Alhassan ta goyi bayan Atiku na zama Shugaban ƙasa

Ministan ta kira tsohon mataimakin shugabann ƙasa da “shugaban ƙasa” in Allah ya yarda 2019

Ministar harkokin mata Aisha Alhassan tana goyon baya Atiku Abubakar ya zama shugaban ƙasa a zaben 2019.

Tsohuwar yar takarar gwamna na jihar Taraba ta faɗi haka a ziyarar da yan jam'iyar APC na jihar Taraba suka kai ma tsohon mataimakin shugaban ƙasa.

A cikin bidiyo wanda aka wallafa a intanet ranar talata 5 ga watan Satumba, ministan tare da tawagar yan jam’iyar APC na jihar Taraba suna mara ma Atiku wajen zama shugaban kasa.

Aisha tana cewa “ Mai girma, baban mu, shugaban kasan mu in Allah ya yarda 2019. A gaban ka mutanen ka ne magoya bayan ka har abada mutanen jihar Taraba”.

ADVERTISEMENT

Ta kara da cewa “sun zo ban girma da gaisuwar sallah tare da yi maka murna na wannan daukakar da Allah ya kara maka, domin daukaka Allah ya riga yayi maka. Don wannan kari shine muka gan faduwa ta zo dai dai da zama, za’aje godiya shine muka ce toh dole ayi da mu”.

Atiku ya fadi a takarar da yi na zaben 2007 wanda tsohon shugaban kasa marigayi Umaru Musa Yar’adua yaci.

Kuma bai  ci nasarar zama dan takarar jam’iya a zaben 2011 da 2015.

Ga bidiyon nan kasa.

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT