Pulse.ng logo
Go

Khalifa Isyaka Rabiu Za'ayi jana'izar marigayi ranar Juma'a

Marigayin ya rasu ne a asibiti dake birnin London yammacin ranar litinin 7 ga wata bayan wata rashin lafiya da ya sha fama da ita.

  • Published:
Khalifa Isyaka Rabiu ya rasu yana da shekara 90 a duniya play

Khalifa Isyaka Rabiu ya rasu yana da shekara 90 a duniya

(DailyNigerian)

Za'ayi jana'izar fitaccen malamin adini kuma hamshakin dan kasuwa, Khalifa Isyaka Rabiu ranar juma'a 11 ga watan Mayu.

Wannan labarin ya fito ne a wata takardar sanarwa da iyalan marigayin suka fitar a garin Legas ranar laraba 9 ga wata.

Marigayin ya rasu ne a asibiti dake birnin London yammacin ranar talata 8 ga wata bayan wata rashin lafiya da ya sha fama da ita.

Ya rasu yana da shekaru 90 a duniya kana ya bar mata da yara 42 da jikoki.

Labarin rayuwar sa

Marigayin, fitaccen malamin addini ne kuma shahararren dan kasuwa ne wanda ya kafa kamafanin Isyaka Rabiu and Sons.

Cikin yaran sa akwai Nafiu Isyaka Rabiu da Alhaji Abdulsamad Isyaka Rabiu, shugaban kamfanin BUA da Nafiu Isyaka Rabiu shugaban kamfanin jirgin sama ta IRS.

Marigayi Khalifa Isyaka Rabi'u ya samu daukaka a rayuwarsa ta fannoni da dama.

Ya yi fice a fagen karatun Alku'ani da yi masa hidima abin da ya sa ake masa lakabi da "Khadimul Qur'an".

Ya kuma shahara wurin kafa makarantu da masallatai musamman a birnin Kano da kewaye.

Daga bisani kuma an nada shi Khalifan Darikar Tijjani a Najeriya saboda irin gudummawar da yake bayarwa a wannan fage.

Do you ever witness news or have a story that should be featured on Pulse Nigeria?
Submit your stories, pictures and videos to us now via WhatsApp: +2349055172167, Social Media @pulsenigeria247: #PulseEyewitness & DM or Email: eyewitness@pulse.ng. More information here.