Dan gidan sarauniyar Ingila mai jiran gado, Yarima Charles, ya kawo ziyara Najeriya ranar Talata 6 ga watan Nuwamba.

Hadimin shugaba Buhari kan kafafen watsa labarai na zamani, Bashir Ahmad, ya sanar da labarin saukar sa a shafin sa na Tuwita.

Basaraken ya sauka birnin tarayya, Abuja, tare da uwar gidan sa Camilla.

Ya samu tarba daga shugaban kasa Muhammadu Buhari tare da sauran ma'aikatan fadar sa.

Gabanin zuwansa Najeriya, yariman ya kai ziyara kasar Ghana da Gambia duk a cikin rangadi da yake zuwa kasashen yammacin Afrika.

Basaraken zai kuma kai ziyara jihar Legas inda daga nan zai bar kasar ranar Alhamis. Wannan shine karo na farko da zai karo ziyara kasar tun cikin shekarar 2006.

Yariman zai yi jawabi kan rikice-rikice dake faruwa a kasar tare da yin karin haske kan yadda za'a karfafa alakar Najeriya da Birtaniya.

Yariman tare da uwar gidan sa zasu kammala ziyarar tasu ranar 14 ga watan inda zasu koma gida gabanin bikin cika shekara 70 a duniya na basaraken.