Pulse.ng logo
Go

Yan shi'a da jami'an tsaro Hargitsi a garin Abuja, yan sanda sun tarwatsa gangamin yan shi'a (Bidiyo)

Wannan ya biyo bayan yan sandan sun hana mabiyan gudanar da gangami  a daidai harabar unity fountain kamar yadda suka saba

  • Published: , Refreshed:
Police cracks down on Shiites protester demanding El-Zakzaky's release play

Protesters attacked by police in Abuja

(Twitter/@GbemiDennis)

Labari ya bayyana cewa ana hargitsi tsakanin mabiya akidar Shi'a da jami'an rundunar yan sanda a garin Abuja.

Hargitsin ya tayar da tarzoma a dai dai Unity fountain dake nan Maitama inda kamar yadda wani shaida ya sanar, yan shi'a suna ta jifar jami'an tsaro da duwatsu yayin da suma jami'an suke watsa masu ruwa da kuma barkonon tsohuwa.

 

Kamar yadda labari ke yawo a kafafen sada zumunta, haya-gagan ya haifar da tashin hankalin ga zukatan al'ummar dake yankin ganin yadda ake jin karar harbin bindiga da kuma barnar da ake yi sakamakon jifa.

Wannan ya biyo bayan yan sandan sun hana mabiyan gudanar da gangami  a daidai harabar unity fountain kamar yadda suka saba.

Sakamakon arangama da suka yi da jami'an tsaro a makon da ta gabata, yan sanda sun kama Deji Adeyanju daya daga cikin masu taimaka ma yan shi'a wajen bin hakkin su.

Police cracks down on Shiites protester demanding El-Zakzaky's release play

Protesters attacked by police in Abuja

(Twitter/@GbemiDennis)

 

Suna gangamin ne don yunkurin sakin jagoran su Ibrahim El-zakzaky wanda har yanzu gwamnati ta garkame shi duk da damar da kotu ta bayar na a sake shi.

Gwamnati da El-zakzaky

A cikin shekara 2016 mai shari'a Gabriel Kolawole ya bada dama na a sake shi bayan gwamnati ta cigaba da tsaran shi kan dalilin kare lafiyar shi.

Shekara biyu kenan da kai hari jagoran mabiya akidar shi'a na nijeriya a gidan sa dake Zaria wanda yayi sanadiyar kashe yaran sa uku da dinbim mabiyan sa. Bayan harin da sojoji suka kai mai sun kuma kama shi wanda har yanzu ana tsaran shi duk damar da kotu ta bayar.

Sojojin sun dirar masu ne sakamakon fito-mu-gama da ya faru tsakanin yan shi'a da tawagar hafsan sojojin Nijeriya janar Tukur Buratai, hanyar shi na barin Zaria yayin da yan shi'a ke gudanar da taron su wanda ya sanya har suka toshe hanya.

Do you ever witness news or have a story that should be featured on Pulse Nigeria?
Submit your stories, pictures and videos to us now via WhatsApp: +2349055172167, Social Media @pulsenigeria247: #PulseEyewitness & DM or Email: eyewitness@pulse.ng. More information here.