Wasu hafizai da suka wakilci Najeriya a gasar karatun Al-qurani sunyi babban nasara a gasar inda suka fito na uku a matakin farko na gasar.

Gasar karatun Qurani na Sarki Salman Abdul'aziz na bana ya kasu zuwa matakai hudu.

Matashi, Amir Yunusa, daga jihar Bauchi shine yazo na uku a mataki na farko (karatun Hizufi 60 da tafsir).

Ibrahim bin Abdullah Al-Saui daga kasar Saudi Arabia shine ya zo a na farko a wannan matakin yayin da shi kuma Malek Othman daga kasar Jordan ya zama na biyu.

Hakazalika Abdulganiy Aminu daga jihar Katsina ya zo na uku shima a mataki na biyu ( Karatun Hizufi 60).

Dan Najeriyan ya raba maki iri daya da Abdulqader Kindi daga Libya kuma an kaddamar da su biyu a matsayin wadanda suka zo na uku a matakin.

A matakin Haitham Safar Ahmed  daga kasar Kenya shine yazo na farko yayin da shi kuma Obaidah Maan Abdul Salam Freihat daga kasar Jordan ya zama na biyu.

Gasar karatun shine na 40 kuma anyi bikin karrama wadanda suka yi nasara ranar Laraba 10 ga wat a nan masallacin Annabi dake Madina.

Gasar wannan shekarar shine karo na farko da za'a gudanar a masallcin kuma yarima Faisal Ibn Salman ya dauki nauyin ta.