Pulse.ng logo
Go

Majalisar dokoki Yan majalisa na shirin daukar mataki kan shugaba Buhari

Shugaban majalisar dattawa Sanata Bukola Saraki ne ya karanta matsayar da suka cimma a zaman da gammayar majalisun suka yi

  • Published: , Refreshed:

Yan majalisar tarayya na shirin daukar mataki kan shugaban kasa game da matsalolin da kasar take fuskanta a halin yanzu.

Majalisar ta yanke wannan shawarar ne bayan zaman da gamayyar majalisar dattawa da na wakilai suka yi.

Majalisun dokokin sun amince da wasu kudurori 12 da suka ce wajibi ne gwamnatin Muhamadu Buhari ta aiwatar da su ko kuma su dauki mataki.

Shugaban majalisar dattawa Sanata Bukola Saraki ne ya karanta matsayar da suka cimma.

Dogara tears IGP apart after meeting Buhari at the Villa play Shugaba Buhari tare da jagororin majalisun dokoki (Presidency)

 

Ya ce majalisun biyu sun amince cewa wajibi ne shugaba Buhari ya dauki alhakin abubuwan da mutanen da ya nada suke yi, sannan ya dauki mataki kan duk wanda ya saba wa doka da yin barazana ga demokuradiyya.

Dangane da matsalar tsaro da kasar take fuskanta, majalisar tace wajibi ne jami'an tsaro su tunkari kashe-kashen da ake yi a kasar, sannan a daina takura wadanda ake wa kallon 'yan adawa ne ko kuma masu bambancin ra'ayi.

Ga kudurorin da yan majalisar suka shigar kamar haka;

*Kawo karshen kashe-kashe a Najeriya

*A daina tsangwama da kuma muzguna wa wadansu 'yan majalisa

*Gwamnati ta rika bin doka da oda

*Shugaban kasa ya dauki mataki kan wadansu wadanda ya nada mukamai

*Ya yi yaki da cin hanci da rashawa tsakaninsa da Allah

*Ya daina sanya baki kan al'amurran da suka shafi majalisar

*Majalisar dokokin kasar za ta fara tuntubar Majalisar Dinkin Duniya don ceto demokradiyyar Najeriya

*Majalisar za ta tuntubi kungiyoyi masu rajin kare demokradiyya don ceto demokradiyyar kasar

*Shugaban kasa ya magance matsalar rashin aikin yi da kuma talauci a kasar

*Duka majalisoshin biyu sun nuna goyon baya ga shugabancin Bukola Saraki da kuma Yakubu Dogara

*Kuma ba sa goyon shugabancin Sufeto Janar na 'yan sanda Najeriya Ibrahim Idris

*Majalisa za ta dauki mataki kamar yadda tsarin mulki ya ba ta dama, idan aka ki yin wani abu.

Wannan zaman ya gudana ne a dai daia lokacin da rashin jituwa ke kara fitowa fili tsakanin gwamnatin Muhammadu Buhari da kuma shugabannin majalisar.

Majalisun suna dai zargin cewa an mayar da su saniyar-ware ne tare da yi musu bi-ta-da-kulli, a gwamnatin da suka taimaka aka kafa.

Do you ever witness news or have a story that should be featured on Pulse Nigeria?
Submit your stories, pictures and videos to us now via WhatsApp: +2349055172167, Social Media @pulsenigeria247: #PulseEyewitness & DM or Email: eyewitness@pulse.ng. More information here.