Pulse.ng logo
Go

Matsalar tsaro Yan bindiga sun tilasta wa yan Zamfara gudun hijira

Wani ganau ya shaida cewa matsalar a halin yanzu ya fi karfin su don haka al'ummar ke gudun hijira.

  • Published:
Zanen jihar Zamfara play

Zanen jihar Zamfara

Hare-haren da yan bindiga ke kaiwa a jihar ya sanya al'ummar Zamfara gudun hijira zuwa jihohi dake makwabtaka da ita.

Tun ba yau ba mazaunan jihar ke fuskantar hare-hare daga yan bindiga da barayin shanu. Banda yan bindiga al'ummar jihar na fuskantar barazanar masu satar mutane.

Lamarin dai ya sanya yan bindiga na bincinkau da rayuwar jama'ar jihar musamman a garuruwa irin su Fura Girke, Majira, Kanawa, Yargeba, Ta-koka, Bargaja, Bundungel, Bantsa, Unguwar Matandada kuma Makera dake karamar hukumar shinkafi.

Wani ganau ya shaida wa wakilin bbc cewa matsalar a halin yanzu ya fi karfin su don haka al'ummar ke gudun hijira.

"Tura ta kai bango, matsala ta taso mana, wanda tun ana yi kauyuka har an kai yau sai a shiga Shinkafi da bindigogi, da manyan makamai a dauki mutum a tafi da shi." Sulaiman Shua'uibu Shinkafi ya shaida wa BBC.

Kan harin da suka kai kwana-kwanan nan Shinkafi mai cewa

Ya kara da cewa "Mutane na kallo ba abin da za su iya yi saboda da manyan makamai suke zuwa."

Bayan ga haka mataimakin gwamnan jihar Alhaji Ibrahim Wakkala yayi kira ga gwamnatin tarayya da ta kawo ma jihar dauki dangane da matsalar da suke fuskanta.

Yayin hakan n ranar juma'a 8 ga watan Yuni yayin da ya kai ziyara kauyukan da hare-haren yan bindiga yayi sanadiyar kauracewar su.

Do you ever witness news or have a story that should be featured on Pulse Nigeria?
Submit your stories, pictures and videos to us now via WhatsApp: +2349055172167, Social Media @pulsenigeria247: #PulseEyewitness & DM or Email: eyewitness@pulse.ng. More information here.