ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Ƙungiyar Likitoci ta buƙaci gwamnatin tarayya da ta duba muhimmancin yarjejeniyar su

Nephro ya nuna taƙaici ganin cewa gwamnati ta kasa biyan alƙawarin da ta ɗauka wajen biyan buƙatun su kuma bata dauki yarjejeniyar da muhimmanci

Ƙungiyar likitoci masu neman kwarewa na ƙasan(NARD) tace zata janye yajin aikin da take indai gwamnatin tarayya zata duba yarjejeniyar biyan buƙatun su da muhimmanci.

Shugaban ƙungiyar reshin asibitin neman kwarraru na jami’ar Abuja Dakta Ucha Nephro ya bayyanar da haka ranar talata yayin da ya gana da kamfanin dillancin labarai (NAN) a garin Abuja.

Nephro ya nuna takaici ganin cewa gwamnati ta kasa biyan alƙawarin da ta ɗauka wajen biyan buƙatun su kuma bata dauki yarjejeniyar su da muhimmanci.

Yace likitocin asibitin neman ƙwararru na jami’ar Abuja basu samu albashin su na watan Janairu, Febreru, Maris da Agusta na 2017.

ADVERTISEMENT

A bisa bayanin shi ƙungiyar ta bukaci gwamnatin tarayya da ta biya bashin da take bin su.

Ya tabbatar ma NAN cewa likitocin asibitin neman ƙwararru na jihar Enugu suma sun shiga yajin aiki bisa ga buƙata  mai kama da nasu.

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT