Pulse.ng logo
Go

Ke duniya! Ya caka wa mahaifiyar sa wuka kan dalilin kudin haya

Kamar yadda shaidu suka bayyana, ya zargi mahaifiyar wanda aka fi sani da Iya Fali da mallakar dukiyar mahaifin shi ba tare da ware nasa kason ba

  • Published:
Nurudeen Bakare ya kashe mahaifiyar sa kan dalillin dukiya play

Nurudeen Bakare ya kashe mahaifiyar sa kan dalillin dukiya

An samu labarin wani magidanci mai suna Nurudeen Bakare wanda ya caka ma mahaifiyar sa wuka har yayi sanadiyar ajalinta.

kamar yadda majiya suka ruwaito, wanda ake zargi da laifin mai shekaru 37 ya far ma gidan mahaifiyar shi ne bayan tsawon shekaru 12 rabon shi da gidanta dake nan layin oremeji na unguwar Illasamaja dake nan jihar Legas.

Kamar yadda shaidu suka bayyana, ya zargi mahaifiyar wanda aka fi sani da Iya Fali da mallakar dukiyar mahaifin shi ba tare da ware nasa kason ba. Yayi barazanar kashe ta inda ita ma ta mayar masa da martani cewa bai isa yin haka ba.

"Abu kamar wasa sai gashi yayi kunnen kashi ga gargadin da mahaifiyar tayi masa. Ya caccaka mata wuka kana yana ta ihu "na kashe ta, na kashe ta".

Ganin yadda Iya fali take kwance a cikin jini rai a mace, matasan unguwa sun dirar masa inda sukayi masa dukar sai-ka-mutu. Cikin halin da ya tsinci kansa ya roki matasa da su taimaka kada su kashe shi, su mika shi ga hukumar yan sanda.

Kamar yadda mai magana da yawun rundunar yan sanda na jihar Legas, Chike Oti ya sanar, an kama shi kuma ana cigaba da tsaron shi a ofishin bincike da basira dake nan Yaba.

Do you ever witness news or have a story that should be featured on Pulse Nigeria?
Submit your stories, pictures and videos to us now via WhatsApp: +2349055172167, Social Media @pulsenigeria247: #PulseEyewitness & DM or Email: eyewitness@pulse.ng. More information here.