ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Aisha Buhari tayi kira ga mata da su koyi sana’a domin dogaro da kansu

Uwargidan tafadi haka a wata takarda da kakakin ta Suleiman Haruna ya fitar ma manema labarai ranar laraba a garin Abuja

Uwargidan shugaban ƙasa Aisha Buhari tayi kira ga mata dake ƙasar da su koyi sana’a domin taimakon kansu da daukar dawainiyar gidajen su.

Uwargidan tafadi haka a wata takarda da kakakin ta Suleiman Haruna ya fitar ma manema labarai ranar laraba a garin Abuja.

Bisa ga takardar matar shugaban ƙasa ta fadi haka ne a garin Bauchi yayin ƙaddamar da wani shiri wanda zai yi wa mata 1,000 horo akan sana’o’i daban daban.

Shirin dai yana daya daga cikin tsare-tsaren Aisha Buhari domin taimaka ma yan ƙasa.

ADVERTISEMENT

A bikin wanda matar gwamnan jihar Bauchi Hajiya Hadiza Abubakar ta wakilce ta, Aisha Buhari tace dole mata su zage damtse a matsayin su na iyaye wajen koyan sana’a.

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT