Hotunan shagalin bikin aurenFatima Ganduje da angon ta Idris Ajimobi wanda yayi  yawo a kafafen sada zumunta, an gan inda suka rungumi juna har hannun mijinta ya kai ga nononta cikin daya daga cikin hotunan.

Sunyi fashin bakin ne ta  hanyar sako da suka wallafa a shafukar su na kafar sada zumunta ta instagram.

Jarumi Ty Shaban ya zartar da nashi bacin rai ga wani jigon masana'antar wanda ya taka rawar gani wajen ladabtar da jaruma Rahama Sadau bisa fitowar da tayi a wani bidiyo inda take rungumar mawaki.

*Auren da gwamna da minista da shugabannin kasa ke zuwa haram suke yi- Sheikh Gummi ya tsokaci game da auren yaran gwamnoni

A cewar shi shi jigon mai suna mallam Nura Hussein wanda yake daya daga kungiyar masu shirya fim yayi shuru kan batun ganin cewa lamarin na yaran manya ne amma inda ga yan fim  ne wanda suke yaran talatawa da an tsawatar dasu.

Yana tambaya kamar haka: "Mallam Nura Hussain Na daya daga cikin masu fada aji a masana'antar shirya Fina finai ta kannywood. Mallam Nura ya taka rawar gani lokacin da jaruma rahama sadau ta fito a wani video Waka Wanda takai har Saida hadaddiyar kungiyar masu shirya Fina finai (moppan)suka dauki matakin ladabtarwa a kanta. TAMBAYA: shin Mallam Nura ba muji yayi wani sharhi akan pre wedding picture Na Fatima GANDUJE da Idris AJIMOBI ba Wanda duniya ta gani karara yana shamata Baki kuma hannuwansa akan nononta? Shin ko fadakarwar an kebe tane akan wasu gungun mutane ne?

Ya kara da cewa bawai ya hakan don ya alakanta jigon da hoton sai don ya tuna masa da irin rawar da ya taka wajen ladabtar da jaruma a matsayin shi na malam amma kuma yayi shuru da faruwar hakan wanda kuma hoton yayi yawo a duniyar gizo.

" Ba Ina nufin alakanta Brother Mallam Nura Hussain bane da hoton bikin Fatima GANDUJE da Idris AJIMOBI, illa rawar da malamin ya taka a matsayinsa Na jarumi wurin tsawatarwa Rahama sadau akan fimdin da tayi...da kuma ladabtar da ita a part 1. To, shine al'umma take kallo yana faruwa a yanzu kuma sunan malamin ya zama Matashiya abin kwatance a part 2 yanzu. kukan kucciya ne kawaii mukeyi."

Shima marubuci Zaharadeen Abdullahi ya koka kan batun inda yayi koke cewa wannan ba dabiar al'adar hausawa bane kuma yin haka yana bata tarbiyar yara.

Yace inda yan fim ne suka yi hakan wanda har yanzu ba'a kama su da yinta ba da malamai sun tsawaita amma daya ke diyan manya ne anyi kunnen kashi kan lamarin.

" Wannan ba dabi'armu baceba Hausa/Fulani anbata mana suna hakkin malamaine su tsawatar!! KALUBALE!! Diyan manya ke bata tarbiya sai an magana kuce yan film sabida su suka fito daga tsatson talakawa Gayaman sunan film din Hausa daya koyarda hakan??

Shima jarumi Zaharadeen Sani ya goyi bayan marubuci inda ya gasgata sakon da rubutan ya  kunsa a kafar sada zumunta na Instagram.