ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Hotunan shagalin bikin Fatima Ganduje da Idris Ajimobi

So da kauna ya shiga tsakanin yaran gwamnonin jihar Oyo da Kano kuma lokakci yayi har an kai ga ranar bikiin auren su.

So da kauna ya shiga tsakanin yaran gwamnonin jihar Oyo da Kano kuma lokakci yayi har an kai ga ranar bikiin auren su.

Fatima diyar gwamnan Kano Abdullahi Ganduje zata amarci angon ta Idris dan gwamnan jihar Oyo Abiola Ajimobi. Ranar asabar 3 ga watan maris za'a daura auren su da misalin karfe 12 na rana. Kafin nan ga wasu hotuna na shagulgulan biki da suka yi.

An fara shagulgulan ne tun a cikin mako inda aka tsara shirye shirye daban daban tun daga na gargajiya har ga na Larabawa.

ADVERTISEMENT

Daga ganin hotuna masu karatu kuna iya ganin yadda so da kauna ya shiga tsakanin bahaushiya da bayarabe. Duk a shirin bikin za'a gan inda al'adun guda biyu zasu nuna iren iren yadda ake gudanar da bikin aure a al'adance.

Za'a daura auren su a babban massalaci dake fadar sarkin Kano kuma ana sa ran zuwan shugaban kasa Muhammadu Buhari da manyan kusoshi a harkar siyasa da fannoni daban daban.

Hakika garin Kano zata samu manya baki da dama.

Enhance Your Pulse News Experience!

Get rewards worth up to $20 when selected to participate in our exclusive focus group. Your input will help us to make informed decisions that align with your needs and preferences.

I've got feedback!

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT